Gwamnoni Na Tsara Yadda Za Su Ribanya Kudaden Harajin Jihohi


Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar duk da matsalar tattalin arziki da mumnunan halin rashin tsaron da ya kassara miliyoyin jama’a, Gwamnonin Najeriya sun fara ha?ilon ganin an ru?anya harajin da ake kar?a a cikin ?asa har kashi 200%, wato nunki biyu.

Nunki biyu na nufin wanda ke biyan Naira 15,00 a misali, zo zai ri?a biyan Naira 45,000 kenan.

Gwamnonin sun fara wannan shiri ne tare da ha?a baki da Hukumar Kula da Harajin Bai-?aya, wato Joint Tax Board.

Sun fito da wani tsarin rariyar manhaja da suka sa wa suna Data for Tax, ko D4T a ta?aice.

Tsari ne da za a tattara bayanan irin sana’a, yayanin samu da yawan ku?a?en shigar da ?ai?aikun mutane kowane ke samu da na kamfanoni da masana’antu.

“Za a ri?a killacewa tare da taskance dukkan wata hada-hadar ku?a?en da mutum shi ?aya tilo ya yi, ko kuma wanda kamfani ko masana’anta ya yi.

“Za ri?a taskance bayanan ne a Rumbun Tara Bayanan Ku?a?en Haraji da ke li?e da lambar shaidar katin ?an ?asa, wato lambar NIN.

A yayin taron da suka yi ranar Laraba, Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta kar?i kwafen Rahoto daga Shugaban Hukumar Tara Ku?a?en Haraji ta ?asa (FIRS).

Shugaban kuma shi ne Shugaban Kwamitin Ha?akar Tarayya da Jihohi na Tara Haraji, Muhammad Nami.

Sun kar?i rahoton ne dangane da yadda tsarin kar?a da tara haraji na D4T zai yi nasara sosai.

Gwamnonin sun nuna goyon bayan su kan shirin, wanda idan aka fara aiki da shi, a?alla zai ?ara sa a tashi kashi 90 bisa 100 na sama da abin da ake kar?a daga kowane mai biyan haraji.

Sun ce za su ha?a kai da Kwamitin JTB domin ganin an samu ?arin ku?a?en shiga da nunki biyu, ta hanyar nunka wa mutane haraji kashi 200%.

Wa?annan bayanai su na ?unshe ne a cikin takardar bayan taron da Shugaban ?ungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ya sa wa hannu, kuma aka raba wa manema labarai bayan ta.

A wurin taron, gwamnonin sun kar?i rahoto daga jagoran Tsarin Abinci na Majalisar ?inkin Duniya da kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Ku?a?e da Tsare-tsare, Olusola Idowu, a kan Tsarin Inganta Abinci Na ?asa.

Related posts

Leave a Comment