Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya ce muhimman kayayyakin zabe na hukumar an daina kai su babban bankin Najeriya, CBN.
Shugaban INEC din ya ce hukumar zabe ba ta taba samu wata matsala da babban bankin ba tun bayan fara wannan hadakar, amma saboda “halin da ake ciki yanzu”, za a samo wata mafitar.
