Matasan PDP Sun Yi Zanga-Zangar Sauke Secondus Daga Mukami

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu fusatattun matasan jam’iyyar PDP sun mamaye wasu titunan Abuja suna neman a sauke shugaban PDP, Uche Secondus, cikin gaggawa, bisa zargin haifar da matsala ga jam’iyyar.

Matasan karkashin kungiyar ceto PDP daga rushewa, wa?anda daga baya suka tattarru a sakatariyar PDP ta kasa, sun ?auki wannan matakin ne saboda ficewar wasu gwamnoni zuwa APC a baya bayannan.

Matasan suna rike da kati wanda aka rubuta “Secondus Must Go” wato wajibi Secondus ya sauka, a yayin gudanar da Zanga-Zangar, wasu kuma na rike da “Mun gaji da jagorancin ka” “Ba zamu jure cigaba da rasa gwamnoni ba” da dai sauransu.

Menene ainihin makasudin zanga-zangar? Da yake zantawa da manema labarai a sakateriyar PDP, shugaban masu zanga-zangar, Com. Tamunotonye Inioribo, ya bayyana cewa idan Secundus ya sauka daga mukaminsa PDP zata samu hanyar saisaita kanta gabanin za?en 2023.

A jawabinsa, yace: “Muna zarginsa da sanya son rai a cikin jam’iyyar PDP, kuma duk laifinsa ne yasa gwamnoni uku tare da sanatoci da yawa suka fice zuwa APC.”

“Manyan ginshikan jam’iyya da suka ha?a da gwamnonin PDP, kwamitin gudanarwa da kwamitin zartarwa duk ya raba kawunan su.”

Tamunotonye ya kuma zargi shugaban da rarraba jam’iyyar PDP a jihohi sabida son ransa da kuma wani kudiri da yakeson cimma wa.

Wane mataki PDP ta ?auka don magance rikici? Bayan wannan cece-kuce da ake ta samu a PDP, Kwamitin amintattu na jam’iyyar ya kira taro da zummar nemo hanyar warware matsalolin da suka taso. Da kuma matsalolin da wasu ?usoshin jam’iyyar bakwai suka gabatar yayin da suka yi murabus daga mu?amansu a makon da ya gabata.

Related posts

Leave a Comment