Fasa Ma’ajiyar Abincin Hukuma Ba Daidai Ba Ne – Dr Jalingo

Cikin ‘yan awowi kadan da suka wuce mutane sun yawaita tambayar mu game da fasa ma’ajiyar abinci na taimakon Corona da aka a wasu jihohi, da kuma diban abincin, ko saye a hannun wanda ya diba.

Amsarmu ga masu wannan tambayar ita ce dukkan abin da aka tambayar ba daidai ba ne musulmi ya yi shi: Kada ku fasa shagunan gwamnati, kada ku dauki abincin da aka ajiye a cikin shagunan, kada ku saya ko ku sayar da irin wannan abincin.

Lalle bin doka da oda yana daga cikin abin da zai tabbatar wa al’umma babbar maslaharsu da kuma maslahar kasarsu.

Sannan muna kira ga hukumomin da abin ya shafa su dauki matakin gaggawa domin gyara inda suka yi kure domin samar wa Kasa da talakwan kasa mafita mai kyau.
Allah ya taimake mu.

Related posts

Leave a Comment