Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan Hudu Na Sayen Fetur Ga ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Buhari ta amince da ware naira biliyan hudu na man motocin aiki na ‘yan sanda a fadin jihohi 36 na kasar hadi da Abuja, domin inganta ayyukan su.

An ruwaito cewa, ministan ma’aikatar harkokin ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ne ya tabbatar da haka a Abuja a ranar Talata. Ministan ya ce kudin wanda aka ware a kasafin 2021 shi ne karon farko da aka ware wa ‘yan sanda kudin fetur kaso mai tsoka a kasar.

Ya kara da cewa Majalisar zartarwa ta tarayya a kwanakin baya ta amince da Ayyukan Musamman na ‘yan sanda don inganta gaskiya da rikon amana tare da zama karin hanyar samar da kudade don inganta ayyukan ‘yan sanda, a fadin Najeriya.

Da aka tambaye shi lokacin da sabon tsarin albashin jami’an ‘yan sanda wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawari zai fito, sai ya ce umurnin Shugaban kasa ga Hukumar Biyan Albashi ta Kasa don samar da sabon tsarin albashi mai inganci zai fito nan ba da jimawa ba.

Related posts

Leave a Comment