Wata babbar kotu a Abuja ta tabbatar da Ahmadu Haruna Zago na ?angaren Sanata Shekarau a matsayin shugaban APC a Kano.
Al?alin kotun mai shari’a Hamza Muazu wanda ya zartar da hukuncin ya kuma bu?aci ?angaren gwamna Ganduje da ya shigar da ?ara yana neman a yi watsi da shugabancin ?angaren Shekarau ya biya tarar miliyan ?aya, kamar yadda Sha’aban Sharada ?an majalisa tarayya ya shaida wa BBC.
Ya ce kotun ta ce ?angaren shekarau ya gudanar da za?ukan maza?u da na ?ananan hukumomi, kuma zai iya gudanar da na jiha.
