Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa shugaban jam’iyyar PDP na ?asa, Sanata Iyiochia Ayu, ya ce ba shi da shirin sauka daga kan kujerarsa a yanzu ko anan gaba har sai wa’adin shi ya cika.
Sanata Ayu na shan matsin lamba na ya yi murabus saboda yarjejeniyar da aka yi gabanin za?en shi shugaba cewa zai aje aiki idan ?an takarar shugaban ?asa ya fito daga arewa.
Tsohon mataimakin shugaban ?asa, Alhaji Atiku Abubakar, ne ya lashe tikitin PDP na takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani, yayin da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya mara masa baya a matsayin na biyu.
Tun bayan za?en fidda ?an takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP ta wayi gari da sabon rikici wanda har yanzun Atiku da Wike ke nuna wa juna yatsa. Tsagin Gwamna Wike sun jaddada matsayar su cewa tilas Ayu ya sauka daga mu?aminsa, hakan ne babban shara?in da gwamnan zai goyi bayan Atiku a babban za?en 2023.
Amma Ayu, a wani rubutu da hadiminsa na ?anagaren ya?a labarai, Simon Imobo-Tswam, ya fitar ranar Litinin, ya ce ba zai yi murabus ba har sai wa’adin shugabancin sa ya cika.
