Bauchi: Hatsarin Mota Ya Kone Mutum 20 Kurmus

Daga Adamu Shehu Bauchi

Hukumar kiyaye hadura reshen jihar Bauchi ta tabbatar ma da manema labarai cewa mutum ashirin sun kone kurmus ta yadda ba’a iya gane su, a sanadiyar Hatsarin mota da ya auku kusa da kauyen Huturu a kan hanyar Kano zuwa Bauchi a yammacin ranar Talata,

A ta bakin Shugaban Hukumar Yusuf Abdullahi da yake ma Yan’jarida karin haske bayan aukuwar hadari a safiyar Alhamis din nan, yace mutum ashirin da daya 21 ne a cikin motocin guda biyu da sukayi taho mu gama, yace direba ne guda daya ya tsallake rijiya da baya a hatsarin.

Ya Kara da cewa motocin da sukayi taho mu game akwai kirar (Volkswagen Golf 3 wacce take dauke da lambar mota SHD-184-YU da kuma Sharon dauke da mutane makare da kayan masarufi

” Hatsarin ya auku ne a sanadin mummunan gudu da suke shekawa, ko da samun labarin hatsarin ma’aikatan mu suka nufi wurin da hatsarin ya auku, ko da isarsu wurin motocin sun kone amma sai mutum daya Muka samu wanda ya fita daga cikin hatsarin, yana jin jiki a kwance” ya fada

Ya ?ara da cewa ” mutum sha daga 11 daga cikin hatsarin Maza ne da Mata su biyar 5 kana da yara guda hudu, shi wanda ya samu mummunan rauni guda dayan an kaishi asibitin garin Kafin Madaki don bashi kulawa”.

Kana daga bisani yace bayan an kammala bincike da sanin inda suka fito da inda zasu, sai aka kai mamatan makabarta don yi masu
Jana’iza a kauyen Huturu gaba dayan su

Shugaban Yusuf ya gargadi direbobin mota ko wace iri ce da su guji rusa guda kaman zasu tashi sama, domin kare rayukansu dana jama’ar fasinjoji da kuma na al’umma baki daya

Related posts

Leave a Comment