Likafa Ta Yi Gaba: Dangote Ya Zama Na 65 A Masu Kudin Duniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote, ya tsallake matsayi 35 a jerin attajiran duniya na Bloomberg, daya daga cikin manyan attajirai 100 a duniya.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, a cewar Bloomberg, yana da dala biliyan 20.4 kamar yadda a ranar Juma’a 8 ga Yuli, 2022, kuma hakan ne ya kai shi ga matsayi na 65 a mafi arziki a duniya.

Rahoton ya kuma nuna cewa daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa Yuli, Dangote ya samu dala biliyan 1.30, wanda hakan ya taimaka masa wajen barin matsayi na 100 da yake a farkon 2022.

Shi dai wannan jadawali na jeri ne na shekara-shekara wanda ke ba da hoto na dukiyar attajirai ta amfani da farashin hannun jari da farashin musaya.

Akwai sama da hamshakan attajirai 500 da aka gano a cikin jerin wadanda suka hada da Dangote, kuma shi kadai ne dan Najeriya.

Related posts

Leave a Comment