Katsina: Sanatan Mazabar Buhari Ya Koma PDP

Rohotanni da ke zo mana na nuni da cewar, Sanatan Katsina ta Arewa wanda yake yankin da shugaban ?asa, Muhammadu Buhari ya fito, Sanata Ahmad Babba Kaita ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Rahotanni sun nuna cewa Babba Kaita ya mi?a takardar ficewa daga APC a maza?arsa ta Galadima ‘A’ da ke ?aramar hukumar Kankia a Jihar Katsina.

Daga nan kuma an samu wani Video da aka hangi Sanata Ahmed Babba Kaita ya ziyarci jiga-jigan Jam’iyyar PDP na Jihar Katsina a gidan gona na Dattijon Jam’iyyar APC, Alhaji Hamisu Gambo Dan Lawan Katsina.

Hakan dai ya tabbatar da cewar Ficewar Sanatan daga APC ta tabbata zuwa PDP.

Related posts

Leave a Comment