Bauchi: Gwamnati Ta Yi Watsi Da Zargin Dan Majalisa Kan Rushe Gida

Daga Adamu Shehu Bauchi

A ranar Jumma ne daya 1 ga watan Oktoba 2021 gwamnatin Jihar Bauchi ta rushe gidan dan’majalisan tarayya mai wakiltan karamar hukumar Bauchi, Yakubu Shehu Abdullahi kan cewa ya sayi gidan akan rashin bin dokan Jihar da aka sa tun tsohowar Gwamnatin Ahmed Adamu Mu’azu ne.

Inda gwamnatin tayi watsi da wan nan batu tana cewa babu kamshin gaskiya a zargin da Dan’majalisan yake yi na cewa siyasa ce zalla yasa gwamnati ta dauki wan nan matakin na hukuncin rushe gidan kai tsaye.

Dan’majalisar tarayya mai wakiltan karamar hukumar Bauchi Yakubu Shehu Abdullahi har ila yau, ya zargi Gwamna Bala Mohammed na Jihar, yana da hannu dumu dumu, a cewarsa Gwamnan yaje wurin rushe gidan da kansa wanda akayi misalin karfe takwas na dare akan titin Buba Yero Old GRA Bauchi, da kuma zargin soke mallakar filin kamfanin chasar shinkafa da ya gina a Jihar Bauchin.

Yayin da Dan’majalisar yake mayar da bayani ma wasu Yan’jarida a Jihar Bauchi, bayan faruwan lamarin yace Babu shakka Gwamnatin Jihar tana yima Yan’Jam’iyyar adawa bita da kulli sunanbi yayan Jam’iyyar APC suna yi masu barazan da kwace masu mallakansu don gudun adawa, a cewarsa sunsan basu tsinan komai ba.

Alumman gari suma suna tofa albarkacin bakinsu gami da wan nan rikicin filin gida da’aka sayar ba tare da bin ka’ida ba, a cewa gwamnatin Jihar.

Bugu da Kari ta bakin Mai bawa gwamnan shawara kan harkokin watsa labarai Mukhtr Gidado yace Dan’Majalisa Yakubu Shehu Abdullahi bayi nazari ko hangen nesa ba, wajen sayen wan nan gida, yace gidajen da suke wan nan gefen su guda tara ne tun fil azal aka yanke hukuncin baza a sayarda su ba amma kawai rana tsaka sak gashi an fara gini a wan nan wuri.

Saboda jaka Gwamnati ta nemi Jin ta bakin dan majalisar a lokaci dabam dabam, amma yayi kunne uwar shegu da maganan shiyasa gwamnatin ta dauki matakin yin hakan, “duk wanda ya taka doka to doka zata takashi”.Ya jaddada.

Daga karshe Dan’Majalisan yasha al’washin maka gwamnatin Jihar a kotu don a karbo masa hakkin sa.

Related posts

Leave a Comment