Bauchi: Uwargidan Gwamna Ta Rarraba Takin Noman Rani

Uwargidan Gwamnan Bauchi Hajya Aishatu Bala Mohammed ta ja hankalin mata manoma a Jihar da su zage damtse don shiga cikin noman rani gadan-gadan don su ttalafa ma tattalin arzikin kasa da na kansu baki daya.

Tayi wan nan jawabi ne yayin da take rabon takin zamani bugun NPK ga kungiyoyin manoma musamman kungiyoyin mata, don bunkasa noman rani na Shekarar 2021

Kana ta kara da cewa wan shirin na tallafin noma tayi shine domin kungiyoyi suci gajiya don asamu yalwar abinci, tace musamman daya ke yanzu damina ta tasan ma karewa, tare da yahabbaka ci gaban mata a Jihar Bauchi baki daya

Aisha Bala tayi nuni da cewa yadda suke fitar da tallafin na kungiyoyi ne ba na faidaikun mutane bane, a cikin Kungiyar be ya kamata su duba suga waye yafi tsakanin bukatan takin sai shuwagabanin su su basu, ko Kuma wadanda akasan cewa sunannoma Kuma yayan Kungiyar ne sai abasu wani ookaci kuma a bawa Wanda bai samu wan nan ba, saboda haka ayi hakuri da abinda aka samu, a mazaunin somin tabi.

Aisha tayi alkawarin tallafa ma matan da Harkar noman ridi, a cewarta “masu bincike sunyi gwaje gwajen su sun gano ridi yana da alfanu mai yawa sosai, wata gidauniya zata tallafa mata ta bangaren gidauniyar ta Almuhibbah dominnci gaban mata, saboda hakanzamu tallafa maku insha Allah indai lokacin yayi” ,Ta jaddada hakan.

Ton a farko Kwamishinayar mata da walwala da jin dadin yara ta Jihar Hajiya Maryam Gidado, tayi tskachi inda ta Yaba ma Uwar gidan Gwamnan kannwan nan tallafi tace, Mata suna da babbar gudumuwar wajen farfado da tattalin arzikin kasa ta fanin noma ko wani iri ne kuwa, kana yaja hankalin kungiyoyin da suka samu takin da su bama marada Kunya suyi amfani dashi a gonakinsu.

Da take jawabin godiya Hajiya Habiba Shugaban Mata manoma (Women Farmers Association Bauchi) tace su tuni suka rungumi noma a mazaunin babbar hanya ce ta yanke talauci, don haka tace baza suyi wasa ba ko kadan da irin wan nan muhimmim tallafi da Uwar gidan Gwamna ta raba masu, tace tayi al’washin zasu raba takin tsakanin su da Allah duk wanda ya dace su za’aba takin

Ta kare da cewa a hidimar noma su babu gudu babu ja da baya, musamman abin da ya shafi kayayyakin da ake sarrafasu cikin sauki manomi ya samu ribar sa akan kari, ba tare da wani bata lokaci ba.

Daga Adamu Shehu Bauchi

Related posts

Leave a Comment