Daga: HASHIM BADIKKO
Barka da warhaka Mai Girma Kwamishna, tare da fatan kana nan lafiya.
Na saurari jawabi, tare da karanta takardar da ka rabawa ‘?an jarida kan matakan tsaro da kuka ?auka a Jihar Kaduna, wanda zai fara aiki daga yau Alhamis 30/09/2021.
Lallai duk wanda yake zaune a Jihar Kaduna ya san cewa babu wani abin a zo a gani da Hukuma take yi game da sha’anin tsaro. Kowa yana zaune ne cikin ?ar, da kuma zullumi. Babu wanda ya tsira.
Ya Mai Girma Kwamishina! Mafi yawan matakan da kuke ?auka, iyakar su a baki ne, ko kuma a takarda.
Jihar Kaduna tana cikin Jihohin da aka fi satar mutane da kuma garkuwa da su a gaba ?ayan Nijeriya, kuma har yanzu babu wasu matakai na zahiri da mahukunta ke ?auka da Mazauna Jihar ke gani don da?ile wannan ta’addancin.
Mr. Samuel Aruwan! Kada ka manta, lokacin da za a rufe makarantu kwanakin baya a fa?in Jihar Kaduna, kun sanar cewa za ku sanya matakan tsaro kafin ku bu?e makarantun, har wani ?an jarida ya tambayi Kwamishinan Ilmi cewa, ai akwai ?ananan Hukumomin da ba sa fuskantar baraza mai yawa, ko za su iya ci gaba da karatu? Ba na mantawa a lokacin ka yi wuf! (Duk da ba kai aka yi wa tambayar ba), ka ce har su ma za a rufe. Kada a sake tambayar!
An rufe dukkan makarantu a Jihar, har na fiye da zango ?aya na karatu (term), wanda kafin wannan an rufe na kusan watanni 10 a dalilin annobar Korona.
Yanzun da kuka ce a dawo a bu?e makarantun, ba mu ga wani mataki da kuka ce za ku ?auka ba kafin ku sake bu?ewa. Haka yara suka yi asarar karatunsu na (third term), wanda illarsa za ta bayyana a nan gaba ka?an. Allah dai Ya kyauta.
Mai Girma Kwamishina! Ba wannan ne ya sa na yi maka wannan bu?a??iyar wasi?ar ba, abin da ya sa na rubuta maka a wannan karon shi ne, sanarwar da ka fitar jiya a kan hana zirga-zirgar BABURA (Private), ba na haya ba.
A cikin sanarwar an ce; an haramta zirga-zirgar dukkan ababan hawa mai ?afa biyu (Babur), na haya da ma wanda ba na haya ba (private).
Ban sani ba ko Kwamishina, tare da masu ba shi shawara sun yi la’akari da wa?annan abubuwa kamar haka:
- Ya za ku yi da Ma’aikata, ko ?an kasuwan da suka dogara da abin hawansu wajen zuwa aiki, ko kasuwa?
- Ya za ku yi da ?an Makarantar da Iyayensu ke kai su a kan babura, saboda rashin ku?i, ko kuma rashin mota daga inda suke zaune?
- Ya za ku yi da Malaman Makarantar da suka dogara da baburansu wajen zuwa makaranta, tunda ba su da ku?in siyen mota, kuma ba lallai bane su iya samun ku?in zuwa makaranta a kullum, tunda albashinsu ba ya samuwa duk wata?
- Ya za ku yi da masu bu?ata ta musamman, kamar guragu da sauransu, wa?anda ba sa iya motsawa daga inda suke sai da abin hawa?
- Ya za ku yi da dubban masu sana’ar gyaran babura?
- Ya za ku yi da dubban masu sana’ar siyar da kayan babura?
- Ya za ku yi da mazauna ?auyukan da babu motar hawa, kuma babu hanyoyin da za su iya fita daga ?auyukansu, sai da babura?
- Yaya za ku yi da masu ?aukar kayan masarufi daga kasuwanni, ko kuma ?ananan masana’antu zuwa cikin gari, kamar masu ?aukar burodi, ko tumatir, ko gari da sauran kayan miya?
Ina ganin ya kamata duk lokacin da Hukuma za ta ?au wani mataki, ta rin?a tunani mai zurfi, da kuma neman hanyar da za ta iya rage ra?a?in da hakan zai iya haifarwa.
Kuma ina fatan ba za ku manta cewa za?arku aka yi ba. Mulkin Dimokra?iyya ake yi, ba Diktaturiyya ba, ba kuma Mulkin Mallaka ba.
Wannan ba shi ne karon farko da nake rubutawa Gwamnatin Jihar Kaduna Bu?a??iyar Wasi?a kan wasu ?odurorinta da nake ganin ba su dace ba, kuma a ?arshe ta bayyana cewa hasashena ya yi daidai.
Shawarwarina Ga Gwamnati
- Ina bai wa Gwamnati shawara a kan ta rin?a ajiye komai a muhalinsa. Ya kamata a duk lokacin da za a ba wani aiki, a duba wurin da ya kware. Kada a ?auki harkar tsaro a bai wa ?an jarida, alhali akwai kwararrun masana harkar tsaro.
- Duk matakin da za a ?auka a rinka duba sashensa guda biyu (negative/positive).
- Kada a sa siyasa a harkar ilmi, tsaro da lafiyar al’umma.
- Al’umma fa suna cikin mayuwacin hali, kada ku rin?a fitar da policies da kuma ?udurorin da za su ?ara jefa su cikin mawuyacin hali.
- Ku fitar da hanyoyin tallafa wa al’umma, musamman wa?anda suka shiga wani mummunan hali saboda matakan da kuka ?auka, ko kuma yanayi ya sa su a ciki.
Ina fatan za ku duba, in akwai na ?auka; Alhamdu Lillahi! In kuma babu; Alhamdu Lillahi!
Ina fatan Kwamishinan Tsaro na Jihar Kaduna, zai wuni lafiya.
Allah Ya kawo tsaro a Jiharmu ta Kaduna, Nijeriya da ma duniya baki ?aya.
Hashim Badikko.
Alhamis: 30/09/2021.
