Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Yanayi ta yi kira ga iyaye mata su rage amfani da itace wajen girki A cewarta, hayakin itacen na illa ga su da yaransu kuma har kisa yana yi Ministar ta kara da cewa hayakin na da illa ga sararin samaniya.
Ministan ta bayyana cewa hayakin itacen girki na kashe sama da yan Najeriya 90,000, musamman mata da kananan yara a kowace shekara. Ministar Yanayi, Sharon Ikeazor, ta bayyana hakan a Abuja ranar Talata, a taron kungiyar wayar da kai kan girkin zamani.
Ta bayyana cewa: “Dogaro kan itace wajen girki na daura nauyi kan bishiyoyi a daji.” “Wannan na da hadari kan lafiyar masu amfani da shi, musamman mata dake girki tare da yaransu.”
Ta ce shekara bayan shekaru, ma’aikatar yanayi na taimakawa wajen aiwatar da shirye-shiryen samar da hanyoyim girkin zamani domin rage tashin hayakin masu illa ga sararin samaniya.”
