Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar hadimin tsohon gwamnan jihar a lamurran Musulunci Sheikh Halliru Maraya ya ce wadanda suke assasa tikitin Musulmi da Musulmi a Najeriya, basa wa kasar fatan alkhairi.
“Ina mamakin yadda kasar za ta koma da tarin matsalolin addini, babu addinin da yake da karfin tsaida ‘dan takara da mataimakinsa idan cancanta ne abin dubawa wajen zaben”
“Bana tunanin akwai musulmin da zai amince da tikitin takarar Kirista da Kirista. Babu shakka, musulmai za su koka a kan janyo rashin adalcin da aka nuna musu.”
