Gombe: An Shawarci Jama’a Su Taimaki ‘Yan Sanda A Yaki Da ‘Yan Kalare

A cigaba da zakulo hanyoyin magance aika-aikar Kalare da ta sake kunno kai a Gombe, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Gombe ASP Mu’azu Abubakar Mahid, ya ja hankalin Al’ummar jihar Gombe da su rin?a taimakawa Jami’an tsaro da bayanai da zasu taimaka wurin dakile aika-aikan ‘yan Kalare a Jihar.

ASP Mu’azu Abubakar ya ?ara da cewar bayanai da al’umma za su rin?a taimakawa jami’an tsaro dashi za su taimaka sosai wurin da?ile bangar siyasa ta ‘yan kalaren dake addabar jihar musamman babban birnin jihar ta Gombe.

Yana mai cewa da taimakon bayanan da suka samu ne su kayi nasarar gano wuraren zaman ‘yan kalaren inda aka kama da dama daga cikin su, yanzu haka suna tsare.

ASP Mu’azu ya tabbatar da cewar an samu sauki akan aika_aikan ta ‘yan kalare a Gombe saidai yace akwai bukatar al’umma su ?ara ?aimi wurin sa ido da bada rahoton ayyukan ?ata gari ga ofishin jami’an tsaro mafi kusa don daukar mataki..

Related posts

Leave a Comment