Rahotanni daga Jihar Katsina na bayyana cewar Gwamnan jihar Aminu Bello Masari, ya sake jaddada aniyarsa ta jingine siyasa da zaran ya kammala wa’adinsa a 2023, domin fuskantar Ubangiji gadan-gadan.
Gwamnan yace zai koma aikin tallafawa marasa ?arfi domim maida ritayar da yayi abun tunawa a koda yaushe. Masari ya bayyana hakane a wurin kaddamar da gidauniyarsa, AMAYEF, wanda ya gudana a Katsina ranar Alhamis.
Masari yace: “Yayin da shekarar 2023 ke ?ara gabatowa, na za?i jingine siyasa kuma zan koma tallafawa mabu?ata da karawa matasa karfin guiwa. Wannan shine ainihin abinda aka kafa gidauniyar dominsa.”
“Matasa suna da babbar rawar da zasu taka wurin saita goben ?asar nan, musamman a wannan matsanancin yanayin da muke ciki.” “Samun matasa nagari a kowace irin al’umma ya na da ala?a da irin damar da aka samar musu, kuma manyan mutane ya kamata su rinka yin haka domin saka wa mutanen su.” “Wannan shine dalilin kafa gidauniyar Aminu Bello Masari, a matsayin ?aya daga cikin gudummuwa ta ga al’umma.”
Gwamna Masari ya yi kira ga masu ku?i a ?asar nan da su tallafawa al’ummarsu musamman marayu, mata, matasa da kuma masu na?asa domin dogaro da kansu. Masari ya ?ara da cewa gidauniyar zata yi aiki tu?uru wajen samar wa matasa aikin yi domin rage zaman kashe wando a cikin al’umma.
