Babban asibitin ?asa dake birnin tarayya Abuja, ya ?aryata tsohon shugaban hukumar kar?ar ?orafe-?orafe ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimingado, kan cewar yaje asibitin ganin Likita a ranar 10/7/2021.


Idan baku manta ba tun a ranar 10/7/2021 ne dai majalisar jihar Kano ta nemi Muhyi ya gurfana a gabanta, domin amsa tambayoyi kan wasu zarge-zarge da majalisar tace ana yi masa.
Sai dai a wannan ranar Muhyi bai samu halartar wannan kiran ba, sai dai ta hannun Lauyansa ya aikewa da majalisar katinsa na ganin Likita da yace yaje a babban asibitin tarayya dake Abuja.
“A binciken da muka yi, babu wani mara lafiya mai suna Muhyi Magaji a cikin rijistar mu, sannan a asibitin mu babu wani Likita mai suna Dr. Bayo.”
Sannan sashin mu na gwaje-gwaje baya bayar da sakamako a rubuce da hannu, sai dai a buge da inji buga takarda kwamfiyuta.” Kamar yadda asibitin ya aikewa da majalisar jihar Kano.
-Idon Mikiya
