Babu Matsala A Tikitin Takarar Musulmi Da Musulmi – Sarkin Yakin Tinubu

Darakta Janar na kungiyar goyon bayan Tinubu, Abdulmumin Jibrin, ya ce ba matsala ba ne don Musulmi da Musulmi sun samu tikitin takaran Shugabancin kasa.

Jibrin ya ce yayin da jagoran APC, Asiwaju Bola Tinubu, ke neman takarar shugaban kasa a
jam’iyya mai mulki a zaben 2023.

Tsohon dan majalisar ya bayyana haka ne a shirin siyasa a kafar Talabijin na Channels, yana mai Cewa al’ummar kasar nan sun fi damuwa da nagartar mutanen da za su dare mukaman gwamnati.

Jibrin ya ce akwai dubban kungiyoyin dake goyon bayan Tinubu a fadin kasar, inda ya ce aikin da yake jagoranta shi ne kula da sauran kungiyoyin.

Da yake amsa tanbayoyin Tsohon dan Majalisar, ya ce idan jam’iyyar APC na so tayi adalci, to ya kamata
mulki ya koma yankin Kudancin Najeriya.

Shugaban ya bayyana cewa ’yan takara kan fito daga wasu shiyyoyin a zabukan da suka gabata suna adawa da tsarin karba-karba, yana mai jaddada cewa,mutane na da ’yancin tsayawa takara ba tare da la’akari da shiyya-shiyya ba.

Da aka tambaye shi game da makomar yankin kudu maso gabas , ya ce da zarar an mika madafun iko zuwa Kudu, shiyyoyin siyasar yankin suna da damar neman mulki.

Kazalika ya ce ba laifi bane idan Musulmi da Musulmi sun tsaya takaran Shugabancin kasa, inda kuma ya ce Na yarda kuma na fahimci cewa kasarmu tana da taka-tsantsan idan ana maganar siyasa, batun kabilanci da addini.

Related posts

Leave a Comment