Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar a wani jawabi wanda fito-na-fito ne da Gwamna El-Rufai ya yi ga Shugaba Muhammadu Buhari, gwamnan na Kaduna ya bayar da umarni a ci gaba da kar?ar naira 500 da naira 1000 a Jihar Kaduna.
Ya bayar da wannan umarnin a cikin jawabin da ya yi wa al’ummar jihar a ranar Alhamis da dare.
A cikin jawabin, El-Rufai ya ce an ?ir?iro canjin ku?i ne don kawai a hana Bola Tinubu na APC yin nasara a za?en shugaban ?asa, wanda za a yi a ranar 25 ga Fabrairu.
Ya ce shigo da tsarin canjin ku?i rashin tunani ne, domin ya haifar da matsanacin ?uncin rayuwa ga jama’a, musamman talakawa.
“Abin takaicin shi ne wa?anda canjin ya fi ?untata wa su ne talakawan da su ka za?e mu. Canjin ya na yin mummunar barazana ga jin da?in rayuwar su.
“Jama’a sun shiga wani mawuyacin hali, saboda a yanayin da ake, kusan ?wacen ku?a?e za a ce banki ya yi masu. Saboda ga ku?a?en su a banki amma ba su iya cira su sayi abinci, ko su biya bukatun yau da kullum na dole a cikin gidajen su.
El-Rufai ya ce an yaudari Shugaba Buhari kuma Gwamnan CBN da mu?arraban sa ne su ka yaudari Shugaba Buhari, inda ya yarda da su wai tsarin an shigo da shi ne don magance wa?anda su ka ?oye ma?udan ku?a?e domin sayen ?uri’u a ranar za?e.
