Bauchi: Muna Bada Hakuri Kan Hatsaniyar Bogoro – Shugaban Kungiyar Zaar

Daga Adamu Shehu Bauchi

Kungiyar Kabilar Sayawa da aka fi sani da suna Kungiyar Cigaban Zarr, ta fito ta bada al’umman Jihar Bauchi da ma gwamnatin jihar hakuri, kan hatsaniyar da ta barke a karamar hukumar Bogoro, asanadin bikin karrama jigo a yankin mai suna Baba Peter Gonto, a ranar 30 da 31 ga watan disemba 2021 da cewa abin takaici ne, kuma sunyi Allah wadai da aukuwan haka.

Shugaban Kungiyar ta kasa Engr. Iswa Gallah, Shine ya shaida ma manema labarai wan nan bayani a sakatariyar Yan’jarida reshen jihar Bauchi, da yammacin ranar Talata.

Haka nan shugaban ya karyata zargin cewa akwai matsalar tsaro a yankin gabanin fara gudanar da wan nan taro na sayawa a yankin Bogoro da Tafawa Balewa, ya cigaba da cewa Babu kamshin gaskiya a wan nan wasikar takardar da babban dan’siyasa a yankin Kuma tsohon kakakin majalisar tarayya Yakubu Dogara da ya aike ma babban sufeton Yan’sanda na Najeriya.

Hakan sunyi fatali da wan nan batu na Yakubu Dogara, da cewa abun ya jefa al’umman yankin cikin zillumi tun kafin gudanar da bikin, inda da ga karshe, a cewarsu makiya ci gaban yankin suka bannata dukiyan al’umma da tada husuma a ranar gudanar da bikin.

Kana kungiyar ta bai wa masarautar Bauchi tare da mai martaba Sarkin Bauchi. Da masarautar Dass da mai martaba Sarkin Dass kan barnar da akayi masu a kan hanyarsu na zuwa wajen taron, wanda ala’tilas suka juya dasu da tawagarsu.

Tun a farko dai Shugaban Kungiyar Zaar Iswa, ya bayyana makasudin wan nan taro a daidai wan nan lokaci, indavyace sunnshitya karrama ma rigayin ne don irin gudumuwar da ya bayar don raya yankin Sayawa ta kwazon kawo zaman lafiya da sauran al’umman yankin, yace zasu kaddamarvda gidauniya, da kuma littafin da zai kunshi gudumuwar da yarihin Baba Peter Gonto amma, a cewarsa makiyan cigaban yankin suka watsa aniyar wan nan taro da su da masu daukan nauyinsu.

Haka nan ya roki hukumar rundunar Yansandan jihar da suyi kokarin binciki Mai Zurfi don gano wadanda suka jawo asarar dukiya da kuma tada hankalin mutane da bakin da aka gayyato don wan nan babban taro.

Kana daga karshe sun yanawa Gwamnan Jihar Bala Mohammed kan jajircewansa na tura jami’an tsaro don ganin ansamar da zaman lafiya a yankin kananan hukumomin Bogoro da Tafawa Balewa,

Kana kungiyar ta fito karara ta nuna alhinin ta, da cewa babu ruwanta akan wannan mummunan al’amari da ya faru a yankin baki daya.

Related posts

Leave a Comment