Babu Gwamnatin Da Ta Yi Aiki A Najeriya Kamar Ta Buhari – Fadar Shugaban Kasa

Rahotanni daga Uyo babban birnin Jihar Akwa-Ibom na bayyana cewar Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yace gwamnatin tarayya ta kashe Naira tiriliyan 8.9 wajen gina abubuwan more rayuwa a shekarar bara ta 2020.

Yemi Osinbajo ya bayyana haka wajen kaddamar da rukunin gidajen Dakkada luxury estate a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a, 24 ga watan Satumba, 2021.

Farfesa Osinbajo yake cewa ba a taba yin gwamnatin da ta kashe kudi sosai domin samar da abubuwan more rayuwa ba irin ta Muhammadu Buhari.

Osinbajo ya bayyana wasu ayyukan da gwamnatocin tarayya da na jiha suka yi a jihar ta Akwa Ibom daga 2015 zuwa yanzu. Mataimakin shugaban kasar yace aikin titin dogon Legas-Kalaba da aikin tashar ruwan Ibom da gidajen Dakkada da ake aiwatar wa sun gyara jihar Akwa Ibom.

“Tun da aka kafa gwamnatinmu, shugaban kasa ya maida hankali wajen samar da tituna, hanyoyin jiragen kasa, lantarki.” “Duk da kalubalen tattalin da aka samu a shekaru shida, mun fi kowane gwamnati kokari gina abubuwan more rayuwa.”

“Zuwa shekarar da ta wuce, mun kashe fiye da Naira tiriliyan 8.9 wajen abubuwan more rayuwa. A watan da ya wuce majalisar FEC ta amince da aikin jirgin kasan Legas zuwa Kalaba wanda zai bi ta Uyo.” “A karshen shekarar da ta wuce, majalisar FEC ta kuma amince da aikin tashar ruwan Akwa Ibom, bayan rokon da gwamna ya kawo.”

Rahoton yace Farfesa Osinbajo ya yabi gwamna Udom Emmanuel kan cika alkawarin da ya yi na gina gidajen Dakkada, wanda za su kawo wa jihar kudin-shiga.

Related posts

Leave a Comment