A ?o?arin bun?asa harkar noma a Najeriya. Babban bankin ?asa (CBN) ha?in guiwa da gwamnatin Jihar, ta raba tallafin bashin kayan noma ga manoman shinkafa sama da ?ari biyar a garin Kontagora dake Jihar Neja. Bashin kayan noman wa?anda suka ha?a ba, buhun shinkafa, buhunan takin zamani, maganin feshi, injimin ban ruwa, injimin feshi. Domin bun?asa harkar noman shinkafa a cikin ?asa.
?addamarwar wanda ya gudana a jiya alhamis ?ar?ashin jagorancin babban bankin Najeriya, da wakilcin ?ungiyar manoma shinkafa ta ?asa (RIFAN) da wakilin shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar Neja Alhaji Balarabe Kagara, wanda Alhaji Abubakar ?an Usman (Sarkin Bakin Kontagora) ya wakilta.
Tallafin bashin wanda manomar zasu biya cikin shekaru uku, an kuma yi kira ga wa?anda suka ci gajiyar tallafin da suyi anfani dashi kamar yadda ya dace domin anfanar kan su da al’umma.
Dadaman wa?anda suka samu tallafin ne suka bayyana godiyar su, tare da shan alwashin yin anfani dashi domin bun?asa harkar noma a Najeriya. Wanda zai taimaka wurin habbaka tattalin arzikin ?asa.
