Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Ogun na bayyana cewar ?aya daga cikin na kan gaba da ke neman takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ce, shi ne ya zama ja gaba a ya?in neman za?en Shugaba Buhari wanda ya yi nasara a 2015.
Tinubu ya ce shi ne ya bayar da sunan Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari.
Jaridar Dailay Trust ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a masau?in shugaban ?asa a birnin Abeokuta na jihar Ogun, yayin da yake tattaunawa da daliget ?in APC gabanin za?en fitar da gwani na jam’iyyar.
Tinubu ya samu rakiyar gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu da takwaransa na Kano Umar Ganduje da kuma tsohon Gwamnan Borno Kasim Shettima.
