Abuja: An Bukaci Mata Su Tabbata Sun Yi Katin Zabe

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa.

A dai dai Lokacin da Jamiyyun Siyasa a Nijeriya ke ci gaba da Kokarin ganin sun fitar da ‘Yan Takarar Kujerun Mukaman Siyasa Daban-Daban a Kasar, Ita Kuwa Shugabar Mata ta Jam’iyyar NNPP Mai alamar kayan Marmari A Babban Birnin Tarayya Abuja, kira tayi ga ‘Yan Uwanta Mata Su Tabbatar sun Mallaki Katin Zabe.

Hajiya Saudatu Abdullahi tayi Wannan Kirane a lokacin da take Zantawa da Manema Labarai a Abuja.

Saudatu Abdullahi ta ce, Babu Shakka an tafi anbar Mata a baya Musamman a wannan Lokaci a don Haka tace yanzun Lokaci ya yi Da ya Kamata matan su Tabbatar sunyi abinda ya dace don Ganin sun Kwaci yancin su da aka Dade ana tauye musu Musamman ta Bangaren More Romon Dimokradiyya

da take Bayani Dangane da Irin Tsaron da Jamiyyar su ta NNPP tayi wa Mata ta bayyana Cewa akwai tsare tsare da Dama da suka shiryawa Mata kasancewar matan sune ginshikin kowacce Nassara a Siyasan ce Inda ta Kara da Cewa Bama Mata ba Jam’iyyar NNPP a shirye take don Ganin ta Samar da Sauyi a Kasa Baki Daya.

Ta Kuma yi Bayani akan Matsalar Tsaro Inda ta Nuna Cewa lallai matsar Tsaro Babban alamarne da ya Kamata ace izuwa yanzun angano bakin zaren Amma gashi wankin Hula ya Kai Gwamnati Mai ci yanzun Dare ta Kara Nuna damuwarta kan yadda Mata ke Shan Wahala Sakamakon matsar Rashin Tsaron da Ake fama da shi

Daga Karshe ta Tabbatar da Cewa Jamiyyar su ta NNPP ma alamra Kayan Marmari Ita kadaice zata Iya Fidda A’i Daga Rogo Amma tace haka Bazai Tabbata ba sai Kowacce Mace ta Tabbatar tana da katin Jefa Kuri’a.

Related posts

Leave a Comment