An bayyana cewar azumtar azumi a ranar 9 ga watan Dhul- Hajji wato ranar Arfa na kankare zunubin shekarar da ta gabata da wadda ke tafe kamar yadda ya inganta a cikin Hadisin Annabi SAW.
Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya kuma Ministan Sadarwa Dr Isa Ali Pantami ne ya bayyana hakan a yayin da yake tunatarwa ga Musulmi akan muhimmancin ?aukar azumi a ranar Arfa.
Pantami ya bayyana cewar wadannan kwanaki 10 na farkon watan Dhul-Hajji kwanaki ne masu daraja da tsada wanda bai kamata Musulmi ya yi wasa a cikin su ba, domin saboda muhimmancin su Allah har rantsuwa ya yi dasu a cikin Al-kur’ani mai girma.
Minista Pantami ya kuma shawarci jama’ar Musulmi da su dage ta hanyar yin addu’o’i a lokutan bukukuwan Sallah da fatan Allah ya zaunar da Najeriya lafiya yayi maganin matsalolin dake addabar kasar gaba daya.
