Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya bayyana dalilin da yasa majalisar ta tafka muhara kan dokar tura sakamakon za?e ta na’ura, da ake ta cece-kuce akai.
A ranar Alhamis da ta gabata ne Sanatocin suka cimma matsaya cewa “Kafin INEC ta aiwatar da tura sakamakon za?e ta na’ura sai hukumar NCC ta tabbatar da ingantaccen sabis na yanar gizo kuma yan majalisa sun amince.”
Lawan ya bayyana cewa majalisar da yake jagoranta ta cimma wannan matsaya ne domin kare muradun sama da rabin ‘yan Najeriya, wa?anda ba za’a ?irga ?uri’un su ba idan aka aiwatar da dokar kai tsaye.
Shugaban Majalisar ya fa?i haka ne yayin hira da yan jarida lokacin da yakai ziyara maza?arsa ta Yobe ta arewa a jihar Yobe, domin ganawa da jama’arsa.
Majalisa ta amince da gyaran kundin dokokin za?e Da yake jawabi dangane da amincewa da dokokin za?e da aka yiwa garambawul, Sanata Lawan, yace: “Nayi farin ciki mun amince da gyaran dokokin za?e duk da wasu na ?orafin matsayar da muka cimma wa da kuma wadda majalisar wakilai ta amince da ita.”
