Kaduna: Sirrin Nasarar Dan Majalisar Mazabar Kawo

Hausawa suka ce yabon Gwani ya zama dole ko shakka babu wannan magana haka take, dole a yaba ma wanda ya dace kuma yake ayyukan shi cikin tsari.

Idan ana maganar Wakili nagari da yankin gundumar Kawo Kaduna ta yi a tarihi, ya zama dole a sanya ?an Majalisa mai ci a halin yanzu Honorabul Yusuf Salihu.

Ba tsawaita bayanai za muyi akan ayyukan alheri da yayi ba, za mu mayar da hankali ne akan wasu muhimman abubuwa biyu da ya yi wadanda sune jigon cigaban kowace al’umma, wadannan abubuwa kuwa sune Inganta rayuwar Mata da Matasa da taimakawa Malaman Addini.

Ya tabbata a tarihin gudummar Kawo daga shekarar 1999 zuwa yau ba a samu wani ?an majalisa wanda ya bada fifiko akan wadannan abubuwa kamar Honorabul Yusuf Salihu.

A binciken da muka gudanar mun gano adadi mai yawa na Mata da Matasa a yankin wa?anda ?an Majalisar ya tsaya musu suka samu ayyukan yi a matakan jiha da kananan hukumomin jihar, kai har da bangaren Gwamnatin Tarayya.

Bayan wannan Honorabul Yusuf Salihu ya bada gagarumar gudummuwa wajen ha?aka sana’o’in matasa a yankin da bada tallafin da ya dace domin haifar da kyakkyawar al’umma nan gaba.

Idan muka waiwayi bangaren iyayen ?asa Sarakuna da Malaman Addini kuwa, Yusuf Salihu ya zama zakaran gwajin dafi wanda ya kusanci wadannan bayin Allah kasancewar muhimmancin da suke dashi cikin al’umma, inda ya bayar da gagarumar gudummawa wajen inganta ayyukan su domin dacewa da samun nasara.

Yusuf Salihu ya kasance wani ?an majalisa mai manufa a majalisar dokokin Jihar Kaduna,bai kasance mai dumama kujera ba, ya dage wajen gabatar da kudurruka gaban majalisa domin amfanar jama’ar maza?ar shi dama jihar Kaduna gaba daya.

Honorabul Yusuf Salihu shi ka?ai ne ?an Majalisa a Majalisar dokokin Jihar Kaduna wanda ya gabatar da kudirin kafa masana’anta wadda za ta koyawa Mata da Matasa sana’o’i sannan ta basu jari domin inganta rayuwar su, wanda ke dab da zama doka.

Wannan ne ya sa Deligates na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna suka amince wa Yusuf Salihu ya zama gwani a Jam’iyyar da zai tsaya mata a babban zaben dake tafe na shekarar 2023 domin ?orawa akan ayyukan cigaba da ya faro.

Related posts

Leave a Comment