Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar rundunar sojin sama ta karyata labarin da wasu kafafen yada labarai suka bayar na cewar an samu hatsarin jirgin saman rundunar a Jihar Kaduna.
A zantawarshi da manema labarai a Abuja jami’in hulda da jama’a na rundunar Kwamanda Edward Gabkwet ya bayyana cewar babu kamshin gaskiya a labarin, domin babu rahoto sahihi da rundunar ta samu akan faruwar hakan.
Rahoton ya bayyana cewar jirgin ya taso ne daga Yola babban birnin Jihar Adamawa zuwa Kaduna domin kai farmaki ga sansanin ‘yan ta’adda dake jihar inda ya gamu da hatsarin.
Sai dai Kakakin rundunar ya bayyana cewar babu wani jirgin rundunar da ya baro Yola zuwa Kaduna a ranar Lahadi, hakan nan babu wani rahoto sahihi na faruwar hatsari da wani jirgi na rundunar.
