Ayyana ‘Yan Bindiga ‘Yan Ta’adda Ishara Ce Ta Ganin Bayansu – Garba Shehu

Rahotanni dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai magana da yawun shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsu ta kusa kawo karshen matsalar ‘yan fashin daji.

Malam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa matakin da gwamnatinsu ta dauka na ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda zai ba su damar tunkararsu gadan-gadan.

A ranar Laraba da ta gaba ne Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta ayyana ‘yan Bindigan matsayin ‘yan ta’adda.

Related posts

Leave a Comment