Dakarun Soji Sun Samu Gagarumar Nasara Kan ‘Yan Ta’adda

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ta kashe wa?anda ta kira ‘yan ta’adda 950, ciki har da shugabannin ‘yan fashin daji Alhaji Auta da Kacalla Ruga cikin wata bakwai da suka gabata.

Mu?addashin shugaban sashen hul?a da jama’a na sojin Najeriya, Manjo Janar Bernard Onyeku, ya fa?a a yau Alhamis cewa sun samu nasarar ce tsakanin 20 ga watan Mayun 2021 zuwa 6 ga Janairun 2022.

Game da kisan jagororin ‘yan fashi, Janar Onyeku ya ce: “An samu nasarar a ranar 3 ga watan Janairun 2022 bayan samun bayanan sirri da ya bayyana wuraren ?uyan shugabannin ‘yan fashi biyu Alhaji Auta da Kacalla Ruga…’Yan fashi kusan 100 aka kashe yayin fafatawar.”

Cikin lokacin da ake magana, rundunar Hadarin Daji ta kashe jumillar ‘yan fashin daji 537 tare da kama 374. Bugu da ?ari rundunar ta ceto mutanen da aka yi garkuwa da su kusan 1,000.

Related posts

Leave a Comment