Kangin Talauci: Rungumar Sana’ar Noma Ne Mafita Ga ‘Yan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya ?i yarda da i?irarin cewa gwamnatin sa ba ta ta?uka komai a fannin Inganta tattalin arzikin ?asa ba.

Ya bayar da amsar cewa mafitar ?asar nan daga ?alubalen tattalin arziki da ku?uta daga talauci shi ne a koma gona a rungumi noma.

Haka ya fa?a a tattaunawar da Gidan Talabijin na Channels ya yi da shi, wadda aka nuna a ranar Laraba da dare.

A cikin tattaunawar sa da Seun Okinbaloye da Maupe Ogun-Yusuf, Buhari bai yarda da wasu al?aluman ?ididdigar da matambayan biyu su ka bijiro masa da su ba, wa?anda su ka nuna masa cewa tattalin arzikin Najeriya tafiyar-kura ya ke yi tun bayan da Buhari ya hau mulki cikin 2015.

Cikin tattaunawar, an baje wa Buhari tantagaryar ?ididdiga da jadawalin tsadar rayuwa da ta?ar?arewar tattalin arziki tsakanin 2015 zuwa 2021.

Related posts

Leave a Comment