Labarin dake shigo mana daga jihar Bauchi na bayyana cewar tsohon kakakin majalisar dokokin tarayya, Yakubu Dogara, ya aike da sakon korafi ga Sufeta Janar na yan sandan ?asar nan, Al?ali Usman, kan yunkurin da ake na kashe shi.
Ya kuma yi zargin cewa baya ga shi, masu mummunan nufin na harin rayuwar wasu mutum uku, cikin su har da shugaban CAN na ?aramar hukumar Tafawa ?alewa.
Dogara, wanda ke wakiltar maza?ar Dass/Tafawa Balewa/Bogoro, ya fa?i haka ne a wata takardar ?orafi da ya tura kai tsaye ga shugaban ‘yan sanda na ?asa.
Ya tura kwafin takardar ga Mai ba da shawara kan tsaro, Darakta Janar na hukumar tsaron farin kaya DSS, kwamishinan yan sandan jihar Bauchi da Daraktan DSS na Bauchi.
Takardar na ?auke da ranar 18 ga Agusta, 2022 da kuma taken, “Kira domin gudanar da bincike kan safarar bindiga tsakanin Insifekta, Dakat Samuel, Inspector Auwalu Mohammed da Barau Joel Amos (Sarkin Yaki).”
“Lamarin na da ala?a da amsa laifin Barau Joel Amos, inda ya nuna cewa ya nemi sayen bindiga da nufin hallaka ni da wasu mutum uku.”
Dogara ya kara da cewa yan sanda uku da ya ambaci sunayen su a sama, yanzu haka suna nan ana binciken su kan zargin kokarin siyar da bindiga ga ?aya daga mutanen maza?arsa.
?an majalisar ya ce bindigar da ake magana akanta, a bayanan ?an maza?arsa da ya amsa laifinsa, ya nemi mallakarta ne da nufin hallaka shi da wasu mutane uku.
“Ina mai jawo hankalinka kan wannan batun da na ta?o wanda yanzu haka yake kan teburin DCP na sashin binciken manyan laifuka a hukumar yan sandan Bauchi.” “Ina ganin labari ya zo gare ka saboda batun ya shafi satar makamai kuma wa?an da ke da alhakin tsare makaman ne ke da hannu da kuma mutum ?aya daga ?an maza?ata, Barau Joel Amos, wanda ya nemi siyan bindiga daga jami’ai.”
“Na shiga damuwa bisa rashin wata shawara daga hukumar yan sanda game da barazanar da ake wa rayuwarmu, wacce zata bamu damar ?ara tsaurara tsaro a tare da mu ko kula da motsin mu.”
Daga ?arshe, tsohon kakakin majalisar wakilan ya roki shugaban hukumar yan sanda na ?asa da a ?auki lamarin dagaske, bai kamata a barshi haka nan sakaka ba.
