Kano: Malamai Shida Sun Rasu A Hanyar Da’awa

Rahotannin da su ke iske mu yanzu-yanzu sun baiyana cewa malamai shida ne su ka rasu a ha?arin mota a kan hanyar su ta dawo wa daga Karamar Hukumar Sumaila, Jihar Kano bayan sun je musuluntar da maguzawa, wato da’awa kenan da harshen larabci.

Wata majiya da ga Imamu Malik Foundation, gidauniyar da a ?ar?ashin ta ne malaman su ke zuwa da’awar, ta ce dukka malamai, shidan wa?anda kuma su ne jagororin da’awar, sun rasu.

A cewar majiyar, a yau da safe ne dai malaman, har ma da wasu ?aliban su, su ka tafi Sumaila ?in domin musuluntar da maguzawa.

Sai dai majiyar ta ce ba su samu labarin cewa ?aliban sun rasu ko sun ji raunuka ba, amma ta tabbatar da cewa malaman duk sun rasu.

Ta ce Mallam Al?assim Zakariyya, shine jagoran tafiyar, shi ma ya rasu.

“Yanzu haka muna can Imamu Malik Foundation a unguwar Dakata, muna jiran sauran ?alibai su karaso sai mu wuce gidan Sheikh Al?assim Zakariyya, inda a nan ne za a yi musu jana’izar,” in ji majiyar, wacce ta nemi a dakatar sunan ta.

Da mu ka tuntu?i Kakakin Hukumar Kare Hadarurruka ta ?asa, FRSC, a Kano, Abdullahi Labaran ya ce har yanzu dai basu samu labarin ba amma zai bincika.

Daga Daily Nigerian

Related posts

Leave a Comment