Rahotannin dake shigo mana daga birnin Abeokuta na Jihar Ogun na bayyana cewar tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo ya ce ba tattaunawar siyasa suka yi da ?an takarar shugabanci kasa na Jam’iyyar APC ba, Bola Ahmed Tinubu.
Obasanjo ya gargadi magoya bayan Bola Tinubu kan ya?a cewa ya marawa takarar Tinubu baya a ganawar sirri da suka yi a gidansa da ke Abeokuta a ranar Laraba.
Ya ce ya?a irin wadannan labarai marasa tushe na lahani ga ‘yan siyasa irinsu Tinubu.
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman ya fitar, kehinde Akinyemi, ya ambato Obasanjo na cewa ganawarsa da Tinubu ta ‘yan uwantaka ce ba siyasa ba.
Wannan na zuwa ne bayan kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a wani taro na APC a Lagos ya na mai cewa ganawar Obasanjo da Tinubu alamar nasara ce garesu a zaben 2023.
Tsohon shugaba Obasanjo dai ya sake jadada cewa shi uba ne ga duk ‘yan Najeriya da matasa da ke cikin matsi.
A baya-baya nan dai tsohon shugaban Kasa Obasanjo ya karbi ba?uncin ‘yan takarar shugaban kasar wa?anda suka fito daga jam’iyyu daban-daban, wa?anda aka fassara ziyarar tasu a matsayin ta kamun ?afa.
Obasanjo ya kar?i ba?uncin tsohon mataimakin shi Alhaji Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP, sai kuma tarbar da ya yi wa Bola Tinubu na Jam’iyya mai mulki ta APC.
