An Zargi Tinubu Da Nuna Wariya Wajen Rabon Mukamai

IMG 20240225 WA0030

Ana ci gaba da nuna damuwa game da na?e-na?en da Shugaban Kasa Bola Tinubu ke yi, inda ake ganin yana fifita abokansa da abokan siyasarsa tare da watsi da ‘cancanta’ lamarin da ya sha alwashin zai magance wajen nada wadanda za su dafa masa.

Sai dai sabanin wannan alkawari, wasu ’yan Nijeriya suna nuna damuwa sosai kan yadda Shugaban yake nada abokai da iyalai da abokan siyasa a kan mukaman mulki, a wasu lokuta ma ba tare da lura da cancantarsu ba.

Baya ga masu sukar rashin lura da cancanta wasu shugabannin jam’iyya wadanda suka yi yaki don nasarar Jam’iyyar APC, suna nuna damuwa kan yadda “aka yi watsi” da su a na?e-na?en da Shugaba Tinubu ya ri?a yi zuwa yanzu.

Wasu ’yan siyasa da manzarta da talakwan Nijeriya, sun ce fatar da suke da ita cewa Shugaba Tinubu zai dauki darasi daga kura-kuran magabatansa ta rushe, lura da jerin nade-naden da ya yi.

Wasu sunayen da suke zuwa idan ana batun na?in son kai a kan Shugaban Kasar sun ha?a da na?a mijin ’yarsa Oyetunde Ojo a matsayin Babban Shugaban Hukumar Gidaje ta Kasa (FHA).

’Yar Tinubu, Folshade Tinubu Ojo ita ce Shugabar Mata ’Yan Kasuwa ta Legas (Iyaloja).

Sai kuma na?a ’yar Cif Bisi Akande, Temitope Ilori a matsayin Darakta Janar ta Hukumar Ya?i da Kanjamau ta Kasa (NACA) da kuma na?a ?an Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, Umar Abdullahi Ganduje a matsayin Babban Darakta a Hukumar Samar da Wutar Lantarki a Karkara (REA).

Sauran na?e-na?en da suka tayar da ?ura a baya-bayan nan sun ha?a da na Olufemi Akinyelure a matsayin Shugaban Sashin Ayyuka a Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NEP).

Shugaban Kasar ya kuma na?a Muhammad Abu Ibrahim, ?an abokin siyasarsa Sanata Abu Ibrahim a matsayin Babban Sakataren asusun bunkasa noma na ?asa NADF.

An ce masu ruwa-da-tsaki a jam’iyyar ba su jin da?in salon na?e-na?en na Tinubu ba tunda ya zama Shugaban Kasa.

Related posts

Leave a Comment