Zazzabin Rana Zai Shafi Ganin Watan Karamar Sallah – Masana

Hukumar nazari da binciken sararin samaniya na Kasar Amurka “National Aeronautics and Space Administration” (NASA) tace ranar Litinin 8-4-2020 ( nan da kwanaki biyu) duniyarmu na Earth zata fuskanci mafi tsananin zazzabin Rana (Sun Eclipse)

Kamar yadda sakamakon binciken NASA ya nuna, duk bayan shekaru 364 duniyar mu tana samun irin wannan zazzabi mafi girma da tasiri da yake jikkata Rana

Mutanen duniya da suka rayu shekaru 364 da ya wuce sunga irin zazzabin, to bayan anyi wannan na ranar Litinin idan Allah Ya kaimu ba za’a sake fuskantar zazzabin Rana mai girma da yake shafan duk duniya ba sai bayan wasu shekaru 364 (Idan Allah bai tashi Alqiyama ba kenan)

Hukumar NASA sunce Rana zata rasa haskenta da kaso 90 cikin 100 na tsawon awanni 5 zuwa 7, ba zamu ga hasken Rana ba, duniyarmu zatayi duhu (SubhanalLah)

Zazzabin ranar zai shafi batun ganin watan Shawwal ranar Litinin idan mun kai azumi 29 kenan, saboda a cewar Geographers wai Wata yana zukar hasken rana ne, to idan ya kasance Rana tayi zazzabi a ranar to ganin sabon jinjirin watan Shawwal zai zama da wuya.

Related posts

Leave a Comment