Watanni takwas bayan da majalisar dattawa ta ki amincewa da shi, rahotanni sun ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai fara ta?addama da gwamnatin Bola Tinubu Duk da cewa suna jam’iyya ?aya.
Rahotanni sun bayyana El-Rufai na sa ran wanke sunansa daga zargin cewa yana da hatsarin tsaro wanda ya hana shi samun mu?amin minista a baya.
Tsohon gwamnan yana son wanke kansa ne bayan da wasu masu sharhi suka ce zai ?alubalanci sake tsayawa takarar Shugaba Tinubu a 2027.
Rahotanni sun ce na kusa da El Rufa’i sun bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta wula?anta tsohon gwamnan a bainar jama’a.
Rashin samun mu?amin na El-Rufai ya ba na kusa da shi mamaki duba da irin rawar da ya taka wajen sanya gwamnonin Arewacin Najeriya suka marawa Tinubu baya a lokacin za?en 2023.
An ambato wani na kusa da El Rufai yana cewa: “Kuna tunanin cewa Mallam zai bari wannan tambarin ya tsaya a kansa? Ina mai tabbatar muku da cewa zai wanke sunansa a gaban kotu.”
