An Zargi Dakarun Soji Da Bu?e Wa Masu Zanga-Zanga Wuta

A daren ranar Talata ne aka zargi dakarun soji da budewa fararen hula wuta yayin taron gangamin zanga-zanga a yankin Lekki a jihar Lagos domi a tarwatsasu bayan sanar da saka dokar ta baci.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da cewa gwamnatinsa ta fara bincike a kan harbe-harben Lekki na daren ranar Talata, domin gano gaskiyar lamarin bu?e wutar.

Sanwo-Olu ya bayyana cewa gwamnati zata yi amfani da faifan bidiyon da na’urar sa-ido (CCTV) ta nada domin gano gaskiya.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, Manjo Janar John Enenche, kakakin Rundunar tsaro ta ?asa, ya ce har yanzu zargin rundunar soji ake yi.

Janar Enenche ya bukaci ‘yan Najeriya su zauna lafiya, su bi doka, su kuma jira sakamakon da kwamitin bincike zai fitar.

“Muna da hotuna da faifan bidiyo na abubuwan da suka faru, mun gano na karya da ake yadawa daga cikinsu. “Jama’a su jira sakamakon da kwamitin bincike zai fitar, gaskiya Za ta bayyana, amma yanzu ba zamu ce komai ba saboda hakan zai iya tauye binciken da ake kan yi,” a cewarsa.

Related posts

Leave a Comment