Shugaban kamfanin sadarwa na ATAR, kuma mamallakin gidan talabijin na Liberty da Rediyon Liberty zangon FM da ke Abuja da Kaduna da Kano Dakta Ahmed Tijjani Ramalan, ya taya shugaban kasa, kuma kwamandan askarawan Nijeriya shugaba Muhammadu Buhari da daukacin ‘yan Nijeriya murnar cikar Nijeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai.
A cikin wata sanarwa da aka fitar daga Helkwatar kamfanin ATAR da ke Abuja, Dr Ahmed Tijjani Ramalan ya jinjina wa ‘yan Nijeriya na gida da mazauna ketare, dangane da yadda su ke ci-gaba da biyayya tare da gudanar da harkokin su na yau da kullum duk kuwa da tarin kalubalen da ake fuskanta.
Dakta Ahmed Tijjani Ramalan, ya ce a matsayin su na jagoran sauran kafafen yada labarai musamman sahen Hausa da Turanci a Arewancin Nijeriya, kafafen Liberty za su cigaba da bada gudunmuwa ta fuskar wayar da kai da ilimantarwa da kuma nisahadanr da ‘yan Nijeriya da ingantattu kuma kayatattun shirye-shirye.
A karshe ya yi wa abokan huldar kafafen yada labarai na Liberty albishir da cewa, za su ci gajiyar garabasar rangwamen farashin tallace-tallace a dukkan kafafen har zuwa karshen watan Oktoba na shekara ta 2021, a wani yanki na ci-gaba da bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan Nijeriya.
