Hukumar Za?e ta ?asa (INEC) ta ?age dukkan za?u??ukan cike gurbi da ta shirya yi a jihohi 11 na ?asar nan.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, kakakin hukumar, Festus Okoye, ya ce an dakatar da gudanar da za?u??ukan cike gurabe 15 saboda halin rashin tsaro da ake ciki yanzu.
A da an shirya yin za?u??uka shida na sanatoci da kuma tara na majalisun jihohi a ranar 31 ga Oktoba.
Zanga-zangar Allah-wadai da ta’asar ‘yansandan SARS ?ar?ashin yekuwar #EndSARS dai ta riki?e ta zama tarzoma wadda har da kashe rayuka a sassan ?asar nan.
