An tashi baram-baram a zaman da ya gudana a tsakanin gwamnatin tarayya da ?ungiyar malaman jami’o’i ba tare da cimma matsaya ba, lamarin da ke alamta cewar kungiyar zata cigaba da gudanar da yajin aikin kenan da ta lashe sama da watanni 8 tana yi.
?angarorin biyu sun samu sabani a game da hanyar da za a bi wajen biyan malaman jami’a bashin albashi da alawus dinsu. Gwamnati ta na so ta biya malaman da ke yajin-aiki albashin da aka hana su da kuma alawus din EAA ta manhajar IPPIS wanda ASUU ta ke adawa da hakan.
?ungiyar malaman jami’ar a karkashin shugabanta, Farfesa Biodun Ogunyemi ta hakikance a kan cewa malamai ba za su yi rajista da manhajar ba.
Charles Akpan wanda ke magana da yawun bakin ma’aikatar kwadago da samar da aikin yi, ya shaida wa ‘yan jarida an dage zaman sai ranar Litinin. Mista Akpan ya ce dakatar da zaman da aka yi, zai ba ‘ya ‘yan kungiyar ASUU su zauna su yanke shawara game da yadda za a biya su wadannan kudi.
Gwamnati ta amince ta biya Naira biliyan 40 da malaman jami’a su ke bi bashi a matsayin alawus din karin aikin da su ka yi tun Nuwamban 2019.
Daga cikin wannan kudi, gwamnatin tarayya za ta soma bada Naira biiliyan kafin 6 ga Nuwamba. Idan za ku tuna, kun ji cewa za a biya sauran kudin daga baya, sannan za a saki N20bn a farkon 2021, za ayi amfani da kudin wajen bunkasa jami’o’i.
