An Tabbatar Da Usman Alkali A Matsayin Shugaban ‘Yan Sanda

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da nadin Usman Alkali Baba a matsayin babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya.

A ranar 6 ga Afrilu ne Buhari ya nada Usman Baba a matsayin mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sanda, bayan kammala wa’adin tsohon shugaban ‘yan sanda Muhammad Adamu.

An yanke hukuncin ne a taron hukumar wanda shugaba Buhari ya jagoranta a ranar Juma’a, 4 ga watan Yuni, a Abuja.

Ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi, ya tabbatar da ci gaban ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a karshen taron.

Related posts

Leave a Comment