Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministar Ayyukan Agaji, Jin?ai da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq ta bayyana cewa kwanan nan za a ?ara ?aukar matasan N-Power 400,000.
Ta yi wannan albishir ne ranar Laraba a Kano, lokacin da ta ke jawabi wurin rufe kwas ?in horas da matasa fasahar N-Knowledge a Kano, wa?anda aka kammala horar da su a ?ar?ashin Rukunin C.
Minista Sadiya ta ce ?arin matasa 400,000 ?in da za a ?auka duk su na cikin matasa miliyan ?aya da Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a samar wa tudun-dafawa a ?ar?ashin shirin N-Power.
“Shirin Kashi na C1 ya ?unshi matasa 510,000, sai Kashi na C2 da za a ?auka kwanan nan, su kuma 400,000 ne.” Inji Minista.
Sadiya ta ce, “Tsarin N-Knowledge shiri ne da aka ?ir?iro shi domin horar da matasa 20,000 fasahar ayyukan kwamfuta masu tafiya da zamani, tare da ba su takardun shaidar ?warewa a fannonin da su ka samu horo a kai, ta yadda za su iya samun ayyukan dabarun fasahar zamani a cikin ?asar nan da sauran ?asashen duniya.
“Kuma za su samu ?warewa sosai wajen dabaru da fasahar ?ir?irar ababen samar da ci gaba da kuma dabarun sana’o’in hannu a zamanance a cikin ?asa ko sauran ?asashen duniya.”
Daraktan Harkokin Ku?a?e Muhammad Sambo ne ya wakilci Minista a bikin yaye matasan su 3,000 da aka yi ranar Laraba a Kano, wa?anda aka za?o daga cikin dukkan jihohin Arewa maso Yamma.
Ya ce a yanzu an horas da matasa 13, 000 a fa?in ?asar nan. Kuma ana nan za a za?ulo cikon ragowar 7,000 daga ko’ina cikin ?asar nan.
