Facebook Ta Bi Sahun Tiwita Wajen Goge Garga?in Buhari Ga Tsagerun Inyamurai

A wani lamari mai kama da na wasan kwaikwayo shima Kamfanin Facebook ya goge gargadin da shugaban kasa Buhari ya yi wa Tsagerun Inyamurai dake neman haddasa ya?in basasa a Najeriya.

Shugaban kasan a ranar Talata yayi barazanar maganin masu kai farmaki ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta kamar yadda sojoji suka yi wa ‘yan tawaye a yakin basasa.

Buhari wanda tsohon Janar ne na Soja ya yi yakin basasa wanda ya lamushe rayukan sama da mutum miliyan daya, a shekarun 1967-70.

“Da yawa daga cikin wadanda ke rashin da’a a yau yara ne da basu san barnar kadarori da rayukan da aka yi ba yayin yakin basasa. Mu da muka yi watanni 30 a filin daga, muka ga yakin basasa, zamu yi muku magana a yaren da kuke fahimta,” yace.

Amma a ranar Juma’a, bayan rahoton da ma’abota Facebook suka dinga kaiwa, Facebook ta cire wallafar daga kafar. “Duba da dokokinmu na duniya, mun cire wallafar da shugaban kasa Buhari yayi a shafinsa na Facebook bayan karya dokokinmu na hana tada tarzoma.

Muna cire duk wata wallafa ta mutum ko kungiya da ta take dokokin Facebook,” kafar tace. Duk da a halin yanzu babu wallafar a shafin Buhari, har yanzu yana nan a na hadiminsa Femi Adesina.

Har yanzu babu tabbacin cewa gwamnatin Najeriya za ta dakatar da aiki da Facebook kamar yadda tayi da Twitter a yau.

Related posts

Leave a Comment