Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewa wani kwararren dan jarida ya ba wa Shugaba Bola Tinubu shawara akan kura-kuran tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
?an jaridar mai suna Mayowa Tijani wanda ke aiki da TheCable ya ce dole Tinubu ya kaucewa wadannan kura-kurai 6 da Buhari ya yi a mulkinsa, matu?ar yana fatan samun nasara a mulkin sa.
An tattaro kura-kuren da dan jarida Tijani ya lissafo kamar haka:
1. Rashin cire tallafin mai Mayowa ya ce rashin cire tallafin mai shi ne babban kuskuren da Buhari ya yi tun farkon karbar mulki a 2015.
2. Rike matatun man Najeriya Mayowa ya ce kuskure na biyu da Buhari ya yi shi ne kashe makudan kudade akan wadannan lalatattun matatar man fetur da ba su tsinana komai ba. Ya ce abin da ya kamata shi ne a siyar da wadannan matatun mai wa ‘yan kasuwa don inganta su.
3. Katsalandan a harkokin shari’a Tijani ya ce duk tsawon shekarun da Buhari ya yi akan mulki ya na bin umarnin kotu idan sun yi masa dadi, idan kuma aka samu sabanin haka to sai ya yi fatali da umarnin.
4. Rashin tsari a tattalin arziki Ya bayyana yadda Buhari ya gagara fitar da ministocinsa har tsawon wata shida a 2015, wanda hakan yasa masu zuba hannun jari suka bar kasar a wannan lokaci. Ya ce Tinubu na garajen fada wa wannan matsalar yayin da ya shafe kwanaki 37 babu ministan kudi da kuma gwamnan babban bankin Najeriya.
5. Soyayyar makanta ga shugabanni So na makanta da ake wa shugabanni ba karamar matsala ba ce kamar yadda Buhari ya fuskanta, hakan ba ya gina kasa. Ya ce: “Makwanni biyu da suka wuce, Ngozi Okonjo-Iweala ta wallafa wasu hotuna yayin wani taro a Faransa, cikin mintuna magoya bayan Tinubu da Peter Obi suka fara fadan wasu abubuwa na takaici.
6. Almubazzaranci da dukiyoyin jama’a Tinubu ya dauki wasu matakai da suke kuntatawa ‘yan Najeriya, kuma sun yi imanin hakan zai rage yawan kashe kudade. Yawan kashe kudade a gwamnatin Buhari ya yi yawa, bai kamata Tinubu ya zama shugaban kasa mai almubazzaranci ba, na kara fada, kada ka zama Buhari.
