Majalisar Kolin Musulunci Ta Yaba El Rufa’i Kan Zaben Kananan Hukumomi

Majalisar ?olin Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta jinjina wa Gwamnatin Jihar Kaduna dangane da yadda ta shirya kuma ta gudanar da za?en ?ananan hukumomi lami lafiya a jihar.

NSCIA wadda ke ?ar?ashin jagorancin Sultan Abubakar III, ta bayyana cewa yadda aka gudanar da za?en ?ananan hukumomi a Kaduna ya nuna nan ba da da?ewa ba, dimokra?iyya za ta hau bisa turba mai inganci a fa?in ?asar nan.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka gudanar da za?ukan ciyamomi da kansilolin jihar Kaduna.

An gudanar da za?en a ?ananan hukumomi 23. Amma kuma an ?age za?ukan a ?ananan hukumomi hu?u saboda dalilai na tsaro, har sai a ranar 25 Ga Satumba.

An buga labarin yadda jam’iyyar PDP ta buga Gwamna Nasir El-Rufai da ?asa a akwatin Maza?ar Unguwar Sarki da ke cikin ?aramar Hukumar Kaduna ta Arewa.

Hakan na nufin PDP ce ta lashe za?en kansilan Maza?ar El-Rufai a Kaduna.

A za?en da aka gudanar a ?ananan hukumomi 23, APC ta lashe 15, ita kuma PDP ta lashe ?ananan hukumomi biyu kacal.

Tun bayan dawowar mulkin dimokra?iyya cikin 1999 dai jam’iyya mai mulki ce ke lashe dukkan za?ukan ciyamomi da kansilolin jihohi.

Wannan ta sa jama’a ke ?orafin cewa kamata ya yi a maida za?ukan ciyamomi da na kansiloli a ?ar?ashin Hukumar Za?e ta ?asa (INEC), maimakon hukumar za?en da gwamnoni ke kafawa, wadda jama’a ba su ganin ta da wata daraja ko ta sisin kwabo.

Dangane da za?en ?ananan Kaduna kuwa, NSCIA ta bayyana cewa hakan na nuna akwai alamun haske a cikin dimokra?iyya nan ba da da?ewa ba.

Majalisar ta tunatar da yadda a baya ake yin ?auki-?ora da tuwo-na-mai-na maimakon za?e a kowace jiha a lokutan za?en ?ananan hukumomi.

Daga nan NSCIA ta yi amfani da wannan dama wajen kira ga ?aukacin Musulmai su ri?a gudanar da komai a bisa gaskiya, adalci, bayar da ‘yanci ga kowa da kuma bin umarnin Allah (SWT).

Related posts

Leave a Comment