Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Majalisar Wakilai ta ce za ta binciki zargin almundahana da ku?i naira Tiriliyan 2.3 a Asusun tallafa wa manyan makarantu (TETFUND) daga shekarar 2011 zuwa 2013.
An cimma wannan matsaya ce bayan amincewa da wata bu?ata da wasu ?an majalisa: Olusola Fatoba, David Fouh da Zakari Nyanpa suka gabatar.
A lokacin gabatar da bu?atar, Fatoba, ya ce tun da aka kafa Asusun Tallafawa Manyan Makarantu a shekarar 2011, asusun ya samu ma?udan tiriliyoyin naira a matsayin kudaden shiga.
Fatoba ya yi zargin cewa “akwai zargin bada?ala a wajen gudanar da ayyukan asusun, musamman a wajen bayar da kwangila da kuma aiwatar da ayyuka.”
“Tsarin aiki a cikin asusun Tallafa wa Manyan Makarantu yana da yawa kuma hakan na iya haifar da rashin sa ido a kan ayyukan da ake yi, tare da raba ku?a?en ba tare da bin diddigin abun da aka yi da su ba, da biyan ku?i ma ?an kwangila duk da gazawar su ta cimma nasarorin da ake bu?ata da kudin.”
Dan majalisar ya ce idan ba a dauki matakan gaggawa ba don bincikar wannan zargin, “lalacewar tsarin makarantu” za ta ci gaba da karuwa.
Majalisar ta kafa wani kwamiti na wucin-gadi da zai binciki zarge-zargen tare da bayar da rahoto cikin makonni hudu domin ci gaba da daukar matakin shari’a.
