‘Yan Daba Sun Yi Wa Dan Sanda Yankan Rago A Kano

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa wasu gungun ‘yan daba sun hallaka wani jami’in ‘yan sanda har lahira a unguwar Yakasai cikin Kano Municipal a yammacin ranar Talata.

Shaidun gani da ido sun shaida cewa, lamarin ya auku ne lokacin da wasu ?an daba suka kai wa wani da ake zargin ?an daba ne hari bayan ya sauko daga Keke Napep a wajen asibitin ?wararru na Murtala Muhammad.

Shaidar ganau ?in wanda ya nemi da a sakaya sunansa ya bayyana cewa mutumin yana saukowa daga Keke Napep ?in suka farmasa da hari.

“Lamarin ya fara ne lokacin da mutumin ya sauko daga Keke Napep, nan da nan wasu ?an daba suka farmasa da makamai.”

“An ?auki lokaci kafin zuwan ?an sanda wa?anda suka kasa korarsu. ?an daban sun koma kan ?an sanda inda suka fara jifarsu da duwatsu.”

“Lokacin da ?an sandan suka yi ?o?arin kaucewa harin da gudun a yi musu ?arna ne ?an sandan ya fa?o nan da nan suka yi kansa inda suka yanka shi har lahira.”

Ya ?ara da cewa a cikin ?an kwanakin nan, ?an daba masu gaba da juna sun sha ba hammata iska a unguwannin birnin Kano

Lokacin da aka tuntu?i kakakin rundunar ?an sandan jihar, SP Abdullahi Haruna, kan lamarin ya bayyana cewa rundunar ba ta samu wani bayani ba amma ana gudanar da bincike.

“Ba mu samu wani bayani ba irin wannan amma muna bincike kan lamarin domin gano ha?i?anin abinda ya faru.” A cewarsa.

Related posts

Leave a Comment