Rundunar ‘yan sandan Iran ta kama wasu ‘yan ?wallon ?afar ?asar bisa zarginsu da shirya bikin shiga sabuwar shekara a birnin Tehran na ?asar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ?asar ya ruwaito.
Wasu daga cikin wa?anda aka kaman sun ha?ar da tsoffin ‘yan wasa da kuma ‘yan wasan da ke taka-leda a yanzu.
Kamfanin dillancin labaran ?asar na Tasnim bai bayyana sunayen ‘yan ?wallon da aka kaman ba, bai kuma yi ?arin bayani game da ?ungiyoyin da ‘yan wasan ke taka wa leda ba.
Rahotonni sun ce wasu daga cikin ‘yan wasan na cikin halin buguwa a lokacin da aka kama su.
